Wata kwararriyar likitar hakoran yara Dr Osarugue Ota, ta ce haihuwar jarirai da hakoransu ko su yi hakora cikin kwanaki 30 da haihuwarsu ba wata matsala bace, kuma hakan bai da nasaba da tsafi.
Dr Ota da ke aiki a asibitin koyarwa na jami'ar Benin ta sanar da hakan a lokacin ba da wani horo ta yanar gizo, inda ya ce madamar aka samu hakan, to ba wata matsala da yaro yake da ita.
Likitar ta ce akwai hakoran da ke fitowa yaro bayan an haife shi, akwai kuma nau'in hakoran da ke fitowa jariri da zarar an haife shi.