An ba da belin Diezani kan kudi Dala 70,000 a Burtaniya

A ranar Litinin din makon nan ne tsohuwar ministar man fetur ta Nijeriya Mrs Diezani Alieson Madueke ta bayyana a gaban kotun Majistare ta Westminster da ke Ingila.

Diezani Madueke dai ta bayyana a gaban kotun ne bisa zargin cin hanci na kudi Dala 100,000.

Sai dai Alkalin kotun Michael Snow ya bayar da belin Mrs Diezani kan kudi Dala 70,000.

Kazalika, Alkalin ya yanke cewa an takaita zirga-zirgar tsohuwar ministar daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safe. Sannan ya zama wajibi ta rika rataya wata alama ta na'urar zamani da za ta rika nuna inda take.

Post a Comment

Previous Post Next Post