Lauyoyin Bazoum na nemar masa hakki a Majalisar Dinkin duniya

Lauyoyin Hambararren shugaban kasar Nijar Bazoum Mohammed da iyalansa karkashin jagorancin Me Seydou Diagne dan asali kasar Sénégal sun gabatar da korafin su a gaban kwamitin kare hakkin dan Adam na majalisar dinkin duniya kan yadda suka ce ana cigaba da rike Bazoum din ne ba akan ka'ida ba kuma hakan ya taka dokar 'yanci dan adam.

Kazalika, lauyoyin sun ce sun shigar da karar sojojin na Nijar a gaban babbar kotun birnin Yamai inda suka bukaci a saki hambararren shugaban da matar sa Hadiza da dan sa Salem wadanda sojojin da suka yi masa juyin mulki suke cigaba da rike wa a fadar shugaban kasar tun ranar 26 ga watan Yuli da ya gabata.

Dama, a tsakiyar watan Satumba nan da ya gabata lauyoyin tsohon shugaban sun shigar da karar hukumomin mulkin sojan Nijar din a gaban kotun ECOWAS inda suke neman kotun da ta mayarwa hambararren shugaban kujerar mulkin sa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ga kamar ana dada kara nisa da matakin amfani da karfin soja da kungiyar ECOWAS ta yi ikirarin dauka a baya kan Sojojin na Nijar domin maido da hambararren shugaban kan kujerar sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post