Hukumomin Nijar sun amincewa Aljeriya ta shiga tsakani kan rikicin siyasar kasar

Gwamnatin kasar Aljeriyar ce ta sanar da wannan mataki na hukumomin mulkin sojan na Nijar na amincewa kasar domin shiga tsakani a cikin rikicin siyasar kasar ta Nijar da ke cikin yanayin juyin mulki

A karshen watan Ogustan da ya gabata ne dai kasar ta Aljeriya ta gabatar da bukatarta ta shiga tsakani a rikicin kasar ta hanyar sulhu tare da nuna adawar ta da dukkan wani matakin soja akan Nijar din da ECOWAS ta yi barazanar dauka domin maido hambararren shugaban

Aljeriyar ta bada shawarar wa'adin watanni shidda (6) a baya na rikon kwaryar kafin shirya zaben da zai maido farar hula

A yanzu dai tuni shugaban kasar ta Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bawa ministan harakokin wajen sa Ahmed Attaf umarnin kai ziyara birnin Yamai nan ba da jimawa domin fara ganawar sharar fage da bangarori da ke da ruwa da tsaki a sha'anin rikicin kasar

Ko daga ranar 23 zuwa 26 ga watan Ogustan shugaban difilomasiyyar na Aljeriya ya kai ziyara kasashen Nigeria, Bénin da kuma Ghana membobin kungiyar ECOWAS domin tattaunawa kan rikicin na Nijar

Post a Comment

Previous Post Next Post