Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP.
Ramalan Yero dai ne Gwamnan jihar Kaduna daga shekarar 2012 zuwa 2015 bayan da maigidansa a wancan lokacin Gwamna Patrick Yakowa ya mutu, ya gaji kujerarsa.
A cikin sanarwar da shi tsohon Gwamnan ya sanya wa hannu, bai ayyana jam'iyyar da ya koma ba.