Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya roki kungiyar kwadago ta NLC da kada ta tafi yajin aiki

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya roki kungiyar kwadago ta NLC da TUC da kada su tafi yajin aikin da suka kudurci aniya a makon gobe.

Kungiyar kwadagon dai ta ware ranar Talata 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta tsunduma yajin aiki na sai baba-ta-gani biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.

Alhaji Sa'ad Abubakar ya ce akwai bukatar a kara ba gwamnatin tarayya dama, kada a yi gaggawar tsunduma yajin aiki.

Ya ce ya shiga cikin sulhu da tattaunawa daban-daban da kungiyar kwadago a lokutta daban-daban, inda ya gano cewa yajin aikin zai kara jefa kasa cikin mawuyacin hali

1 Comments

  1. Gaskiya tafiya yajin aiki ba shine MAFITA ba.Illa dai hakan zai Kara jefa TALAKA CIKIN KUNCIN RAYUWA.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post