Yawan hadiman Gwamna Abba a Kano sun haura 400

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake fitar da sabbin nade-nade na masu taimaka masa na musamman su 116 a fannoni daban-daban.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

Dama dai, a ranar Talatar da ta gabata, Gwamnan ya nada mutane 94 mukamai daban-daban a matsayin masu taimaka masa na musamman.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, da wannan nadin baya-bayan nan, yanzu haka Gwamna Abba na da mataimaka na musamman da hadimai kusan 406.

Da yake kare wadannan nade-nade, Gwamna Abba ya ce yin hakan na da nufin saka matasa sosai a cikin tafiyar da gwamnati da za su taimaka masa ya sauke nauyin da ya dauka na al'ummar Kano.

Daga cikin mukaman na baya-bayan nan, akwai manyan masu taimaka wa Gwamna na musamman SSAs guda 63, sai mataimaka na musamman SAs guda 41.

Bugu da kari, akwai hadimai wato PAs guda 12.

Post a Comment

Previous Post Next Post