Jagoran jam'iyyar adawa ta NNPP a Nijeriya Rabi'u Musa Kwankwaso ya caccaki shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ce Gandujen ba zai iya kai Tinubu ga nasara ba a zaben 2027 mai kamawa.
Kwankwaso da ya yi wa jam'iyyar NNPP takarar ahugaban kasa a zaben watan Fabrairu, 2023 ya ce Ganduje matsala ne a jam'iyyar APC.
A cikin wata sanarwa daga Sakataren yada labaran jam'iyyar NNPP na kasa Hon Yakubu Shendam na mayar da martani ne kan wasu kalamai da aka alakanta su da shugaban jam'iyyar APC Ganduje da aka ce ya ce, Rabi'u Kwankwaso ya saba faduwa zabe.
Jam'iyyar NNPP ta ce duk da zarge-zargen da suka dabaibaye Ganduje, bai kamata ya rika tsoma baki ga harkar mutanen kwarai irinsu Kwankwaso ba. Sanarwar ta kara da cewa wadannan bahallatsar da ake zargin Ganduje da aikatawa a lokacin yana Gwamna ne za su hana shi yin wani katabus a zaben 2027 mai zuwa. Ta kara da cewa muddin Ganduje zai ci gaba da shugabantar APC, tabbaci hakika, jam'iyyar ta mutu.