An yi yunkurin juyi mulki a kasar Burkina Faso

Sojojin da ke mulki a kasar Burkina Faso sun sanar cewa an yi yunkurin hambarar da gwamnatisu.

A cikin wata sanarwa daga sojojin, dakarun kasar sun ce  akwai wasu tsirarun sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki, amma dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

Sojojin da ke jagorantar kasar ta Burkina Faso sun ce masu son sake wani juyin mulkin na son jefa kasar ne cikin hayaniya da rikici na babu gaira babu dalili.

A cikin sanarwar, sojojin sun ce sun yi nasarar kama wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin kamar yadda mai magana da yawun tawagar sojin da ke jagorantar kasar ta Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel ya karanta sanarwar.

Gwamnatin sojin ta ce za ta fadada bincike don gano musabbabin wannan yunkuri na tsirarun sojojin, inda ta kara da cewa abin takaici ne a ce sojin da ya yi rantsuwar zai kare kasarsa, amma ya buge da wannan abu da suka kira aika-aika.

Ta ce ana tsare da sojoji hudu cikin wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin, sannan ana neman karin biyu.

Sojoji dai karkashin jagorancin Capt Ibrahim Traore sun karbe mulkin kasar Burkina Faso a shekarar bara Satumba, 2022, bayan da suka ce matsalar tsaro ta yi kamari.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp