Jami'ar UMYUK ta kori 'lakcarori' da wani ma'aikacinta daga aiki



Hukumar gudanarwar jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina ta sanar da korar wasu malaman jami'ar su biyar bisa samunsu da aikata wasu laifuka da suka ci karo da dokar da ta kafa jami'ar.

A cikin wata sanarwa daga Magatakardan Jami'ar Muhammad Yusuf Abubakar da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce wannan matakin ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa bayan samun wadannan malamai da laifukan da aka zarge su da shi.

Daga cikin wadanda aka kora din, akwai Mr Ayaka Simon Silas na sashen kimiyyar siyasa (PSN 001003) da Abubakar Rabi'u na sashen tsare-tsare (PSN000565).

Sauran su ne Umar Shehu na sashen koyar da tattalin arziki na 'Economic' (PSN 001768) da Nura Hamisu Muhammad shi ma daga sashen koyar da tattalin arziki na 'Economic' (PSN 001664) da kuma Umar Abubakar Aliyu duk dai daga sashen koyar da tattalin arziki na 'Economic' na jami'ar (PSN 000769).

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp