Maulud: Gwamnan Katsina Dikko na son mutane su yi koyi da kyawawan halayen fiyayyen halitta SAW

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya bukaci 'yan Nijeriya daga kowane addini da su kaunaci juna a harkokinsu na yau da kullum.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamna, Ibrahim Kaula Mohammed da ya aike wa DCL Hausa ta ce yin hakan, zai sa a samu zaman lafiya hadin kai da kaunar juna a tsakanin 'yan Nijeriya don samun al'umma daya mai neman makoma daya.

Malam Dikko Umaru Radda a sakon da ya aike da shi don bikin zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta manzon tsira sallallahu ta'ala alaihi wa sallim, na bana, ya bukaci mutane da su rubanya kwazonsu wajen aikata daidai da koyi da halaye na gari na fiyayyen halitta "SAW".

"Manzonmu, manzon tsira sallallahu ta'ala alaihi wa sallim ya yi daban da sauran manzanni, wanda ya gudanar da rayuwarsa cikin kana'a da tausayin al'ummar duniya da tsantsar gaskiya da rikon amana da sauran halayen na ƙwarai". Inji Dikko.

Post a Comment

Previous Post Next Post