Mahaifiya ta kai danta kotu don yana barazanar kashe ta a Kano

Wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu jihar Kano ta tsare wani mutum da aka sakaya sunansa bisa zargin barazanar kisan mahaifiyarsa.

Mahaifiyar yaron dai ce ta maka dan nata kotu bayan da wata zazzafar muhawara ta barke a tsakaninsu.

Mahaifiyar dai ta roki kotu da ta umurci dan nata da ya tashi ya bar mata gida don tsaron rayuwarta.

Sai dai bayan da alkali ya karanta masa laifukan da ake tuhumarsa, dan matar duk ya musanta su.

Ya shaida wa kotu cewa, kawai dai saboda ya rabu da matarsa, kuma yanzu baya da kudi ne ya sa mahaifiyarsa take masa wannan zillar.

Alkalin kotun Khadi Isah Rabi'u Gademi Gaya ya umurci da a ci gaba da tsare yaron har sai ranar 25 ga watan Oktoba inda za a ci gaba da sauraren karar.

Post a Comment

Previous Post Next Post