Gwamnatin Tinubu ta fusata kan kalaman Gwamnan Zamfara na cewa tana sulhu da yan bindiga a sirrance

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya caccaki gwamnan jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, kan ikirarinsa na cewa gwamnatin tarayya na yin ganawar sirri tsakaninta da ‘yan bindiga a jihar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Suleiman Haruna, ya fitar a Litinin din nan.

Sanarwar ta ce gwamnatin Nijeriya ta nuna rashin jin dadinta kan yadda gwamnan ya yi kalaman sakamakon cewa ya fito daga jam'iyyar adawa ta PDP.

Post a Comment

Previous Post Next Post