Farashin buhun siminti zai iya kaiwa N9,000 a Nijeriya

Kungiyar masu harhada siminti ta Nijeriya ta ja kunnen cewa muddin gwamnatin tarayya ba ta tsahirta shirinta na amfani da tsarin zuba kankare a kan titunan da ake ginawa ba, to farashin siminti zai iya kai wa Naira 9,000 a kasar.

A halin da ake ciki dai, ana sayar da jikkar simintin mai nauyin kilogram 59 kan kudi N5,000 ko fiye a wasu wuraren.

Kazalika, kungiyar ta ja hankalin cewa akwai bukatar gwamnati ta sa baki wajen yawan tashin farashin da simintin ke yi a 'yan kwanakin nan ta hanyar kai dauki a masana'antar sarrafa simintin.

Kungiyar a cikin wata sanarwa daga Shugabanta Prince David Iweta da Sakatare Reagan Ifomba, ta yaba wa ma'aikatar aikace-aikace ta tarayya da take kokarin yin amfani da simintin a wajen gine-ginen hanyoyi, sai dai ta ja kunnen cewa yawan amfani da simintin zai sa a rika nemansa a kai a kai da kuma hakan zai sa ya yi tsada a kasuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post