Burin Dikko Radda shi ne kowa ya tsaya da kafafunsa - Abdullahi Garba Faskari


Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Barr Abdullahi Garba Faskari ya ce burin Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda shi ne kowa ya dogara da kansa.

Ya ce yin hakan zai taimaka mutane su samu ingantattar rayuwar da ta dace.

Barr Abdullahi Garba Faskari na magana ne a Funtua a wajen kaddamar da shirin wayar da kan al'umma game da alfanun da ke tattare da tashar kula da shige da ficen kaya ta kan tudu wato Funtua Inland Dry Port a garin Funtua jihar Katsina.

Sakataren Gwamnatin jihar ya ce gwamnatin jihar ta samar da fili murabba'in kadada 77 domin gina wannan tasha a matsuguni na dindindin domin samun ingancin shige da ficen kaya yadda ya kamata.

Ya misalta cewa fadin fili murabba'in kadada 77, shi ne kwatankwacin filin kwallo 77 ta yadda wurin zai wadatar da duk abin aka shigo ko za a fita da shi daga Nijeriya.

Barr Abdullahi Faskari ya ce hakan zai samar wa da dumbin mutane ayyukan yi da hakan zai sa tattalin arzikin jihar Katsina da na Arewa da ma na Nijeriya bakidaya ya bunkasa.

Ya ce dama tuni burin Malam Dikko Umaru Radda shi ne ya ga mutane sun samu hanyoyin da za su dogara da kansu ta yadda gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata domin ta tallafa musu.

Post a Comment

Previous Post Next Post