Kotu ta kwace kujerun ‘yan majalisa uku na PDP a jihar Filato

‘Yan majalisar dokokin da kotun sauraran kararrakin zaben ta rusa zabensu tare da mika nasara ga APC da LP sune Remvyat Nanbol da Agbalak Adukuchill da kuma Happiness Akawu da ke wakiltar Langtang central da Rukuba/Iregwe da kuma Pengana.
Jaridar Daily Trust ta ce wannan na zuwa ne kwana guda kafin kotun ta yanke hukunci tsakanin APC da PDP a zaben gwamnan na jihar ta Filato.

Post a Comment

Previous Post Next Post