Fallen atamfa ya yi sanadiyyar rasuwar wani mutum a Kano


Wani mutum mai shekaru 37 mai suna Usman Ayuba ya riga mu gidan gaskiya a lokacin da ya shiga wata rijiya don dauko atamfar wata mata da ta fada a ciki.

Lamarin ya faru ne a yankin Kawon Maigari na karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Abdullahi ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN, inda ya ce lamarin ya faru ne da yammacin Talata.

Jami'in ya ce sun samu labarin cewa wata mata ce ta bukaci Usman da ya shiga rijiyar domin dauko mata fallen atamfarta da ya fada a ciki.

Bayanai sun ce mutin ya rasu ne ta dalilin karancin iskar shaka a cikin rijiyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post