Ranar sanin makoma a Kano


Ranar Sanin Makoma! Ita ce kalmar da ta kusan yin dai-dai da zama taken wannan rana a wajen mutanen jihar Kano.

Kowanne lokaci daga yanzu, kotun dake sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano za ta yanke hukuncin da zai tabbatar da mafarkin ‘yan “Gawuna is Coming ko kuma Kwankwasiyya zama daram.

Jihar Kano na cikin jihohin da jam’iyyun adawa suka maka jam’iyya mai ci a gaban kotu inda suke nuna shakku game da cin zaben, duk da dai bangaren jam’iyyar NNPP da ta lashe zabe na ganin zaben nasu halastacce ne.

Shin wai mene ne dalilin da ya sa jam’iyyun biyu ke nuna wa juna yatsa a game da sahihancin zaben?

Da farko jam’iyyar APC mai adawa na bukatar kotu ta rushe zaben bisa wasu dalilai da suka hadar da aringizon kuri’a, da kuma rashin chanchantar dan takara Abba Kabir Yusuf da kuma rashin kasancewarsa cikin jerin mutanen da ke neman takarar gwamnan jihar Kano a lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bukaci a mika.

A yayin zaman sauraren shari’ar, lauyan jam’iyyar APC Abdul Fagge ya gabatar da shaidu guda 32 da suka hadar da matsalolin da aka rika samu a gurin tantance masu kuri’a da ma yadda aka daina amfani da nau’urar a wasu gurare a lokacin zaben.

Haka kuma ya gabatar da takardun sakamakon zabe a matakin mazaba da kananan hukumomi, wadanda alkalumansu, suka sha bambam da wadanda hukumar zabe ta jihar Kano ta sanar.

Baya ga kalubalantar sakamakon zabe da aikata ba dai-dai ba, lauyan jam’iyyar ta APC ya kuma kalubalanci ingancin takardun Kammala karatu na gwamna Abba Kabir Yusuf.

Yayin da ya ke mika wa kotu shaidunsa na karshe, Lauya Fagge, ya zargi jamiyyar NNPP da yi wa dokar zabe ta 2022 karan tsaye, kasancewar sam Abba ba ya cikin ‘yan takara, katsam kawai aka gan shi daga sama, ma’ana dai har lokacin da hukumar INEC ta kammala karbar sunayen ‘yan takara jam’iyyar NNPP ba ta aike da sunan Abba a matsayin dan takararta ba.

A binciken da DCL Hausa ta gudanar cikin kundin dokokin zabe ta gano cewa sashe na 72 ya fayyace cewa dole ne jam’iyya ta aike wa INEC rajista da kuma sunan dan takararta kwanaki 30 kafin gudanar da zaben cikin gida.

A cikin bayanin da Lauya Abba ya yi, ya  gano cewa akwai takardun kada kuri’a guda dubu 270 da aka samu sun lalace, kuma babu tambarin hukumar INEC a jikinsu amma duk da haka aka kirga su a matsayin cewa Abba aka zaba, sannan ya ci gaba da cewa hukumar INEC ta ayyana zaben ‘yan majalisar jiha guda 15 a matsayin wadanda ba su kammala ba, kuma an yi su ne lokaci guda da na gwamna, don haka matukar an samu matsala a na dan majalisa ya zama wajibi a samu a na gwamna.

A karshe dai lauya Abdul Fagge na bukatar kotu ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, wato dai kalmar  “INCONCLUSIVE”  da wasu ke ganin kan razana magoya bayan Kwankwasiyya ta tabbata.

                                     Matsayar NNPP

To amma duk wannan dogon turanci da lauyan APC ke yi tamkar dai waka ce a kunnuwan lauyan jam’iyyar NNPP Bashir Tudunwuzurci, wanda ke bukatar kai tsaye kotu ta yi watsi da wadannan hujjoji da ya ayyana a matsayin ba ta lokaci.

A cewarsa, idan aka yi la’akari da irin ratar da jam’iyyar NNPP ta bai wa APC  yawan kuri’un da aka  kada  tabbas cin zarafi ne ma APC din ta shigar da kara.

Lauya Tudun wuzurci ya dage kan cewa sunan Abba na  nan cikin takardar da aka mika wa hukumar INEC kuma an mika ta a kan lokaci kamar yadda doka ta tanada, yana mai cewa tuni kotun koli da ke saurarar kararrakin kafin zabe ta yi watsi da wannan kara ta rashin sunan Abba cikin jerin ‘yan takara.

Kan batun kuri’u fiye da 270 da ba su da tambarin hukumar INEC da APC ke ikirarin an zabi Abba da su, Lauyan ya ce jam’iyyar APC ta gaza gabatar da samfurin takardun a gaban  kotu, kuma babu wata mazaba a fadin jihar Kano da aka sami wannan korafi sai a yanzu ake jin labari.

Sai dai binciken da DCL Hausa ta sake yi kan wannan batu a cikin kundin dokar zabe ta 2022, ta ce ko da babu tambarin hukumar INEC a jikin takardar zabe, matukar kwamishinan zabe ya kirga ta, to tabbas za a dauke ta a matsayin mai inganci.

Lauyan jam’iyyar NNPP ya roki kotun da ta yi watsi da bukatar APC na ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, a cewarsa, idan aka yi la’akari da yawan mutanen da suka fita zaben, babu makawa za a gane ingancin yawan kuri’un da Abba ya samu.

Hukumar dai ta sanar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP  a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’a 1,019,602, abin da ke nufin ya samu nasara kan babban abokin takararsa na jam’iyyar APC Dr Nasir Yusuf Gawuna wanda ya sami kuri’a 890,705. 

Yanzu mutane a cikin da wajen jihar Kano sun zura ido su ga irin hukuncin da kotun sauraran zaben ta yanke. Amma masu sharhi na cewa maganar zargin magudi ba za ta mutu a nan ba, domin babu alamun duk bangaren da hukuncin bai yi wa dadi ba, zai rungumi kaddara ya tari gaba, inda tuni wasu ke cewa komi wuya ko rintsi, da alama kotun koli za ta iya tabbatar da “Gawuna is Coming” ko kuma “Kwankwasiyya Daram”


Post a Comment

Previous Post Next Post