Jigon APC ya lakada wa kwamishina dukan tsiya

Shugaban jam'iyyar APC na wata mazaba a jihar Ondo Mr Olumide Awolumate ya yi bayani tiryan-tiryan dalilin da ya sa ya lakada wa kwamishinar mata da walwalar jama'a ta jihar dukan tsiya.

Ya ce sa'in-sa ce ta kaure tsakaninsu, da ta kai su ga dambacewa da Mrs Juliana Osadahun.

Bayanan da jaridar Punch ta tattara sun ce cacar bakin da ta kai ga kai dukan ta faru ne a wajen rabon kayan tallafin rage radadin tsadar rayuwa a karamar hukumar Arigidi Akoko ta jihar ta Ondo.

Bayanai sun ce jigon na APC Awolumate har ya raunata kwamishina Osadahun a kai. Sai dai rahotanni sun ce tuni uwar jam'iyya ta jiha ta dakatar da wannan shugaban jam'iyya na mazaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post