Nijeriya na bukatar karin azuzuwa 907,769 a makarantun bokon kasar - UBEC

Shugaban hukumar kula da ilmin firamare ta Nijeriya UBEC Dr Bobboyi Oyeyemi ya ce kasar na bukatar karin makarantun boko 20,000 da azuzuwa 907,769. 

Dr Bobboyi ya ce sai an yi hakan sannan a yi nasarar magance matsalar yaran da ba su zuwa makarantun boko.

Shugaban hukumar na magana ne a lokacin da hukumomin da ke karkashin ma'aikatar ilmi ta kasa suke ganawa da ministan ilmi Prof Tahir Mamman a Abuja.

Dr Bobboyi ya sanar da ministan cewa akwai karancin gine-gine da ma'aikata da ake bukatar a cike gibin muddin ana so a yi nasarar samar da ilmi mai inganci ga yara.

Post a Comment

Previous Post Next Post