Babban layin lantarkin Nijeriya ya kara faduwa

Babban layin lantarkin Nijeriya wato 'National Grid' ya sake faduwa, dalilin da ya sa mafiyawan sassan kasar babu hasken lantarki.

Bayanan da Daily Trust ta tattara sun ce layin Delta power plant ne kadai ke da megawatt 41 sai layin Afam da ke da megawatt 1.7.

Hakan ya zo kwanaki biyar da durkushewar babban layin lantarkin da hakan ke jefa sassan kasar cikin duhu.

Har yanzu dai babu takamaiman dalilin da ya sa layin lantarkin ya fadi a wannan karon, amma a wancan karon, ministan lantarki Adebayo Adelabu, ya ce wata gobara ce da ta tashi ta haddasa faduwar layin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp