Kotun sauraren kararrakin zabe ta Tribunal ta soke nasarar da shugaban majalisar dokokin jihar Gombe Abubakar Luggerewo ya samu a zaben da aka yi masa a watan Maris.
Abubakar Luggewo dai na wakiltar karamar hukumar Akko, a majalisar dokokin jihar, a jam'iyyar APC.
Mai shari'a Michael Ugar ya yanke hukuncin cewa a gudanar da zaben cike gurbi nan da kwanaki 30 masu zuwa.