Gwamnatin Dikko za ta dauki nauyin dalibai 'yan asalin jihar Katsina zuwa karatu kasashen waje


SHIRI NA MUSAMMAN DON BAYAR DA GURABEN KARATU ZUWA JAMI’O’IN KASASHEN WAJE GA DALIBAI 'YAN ASALIN JIHAR KATSINA


Mai girma gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya amince da a fara tattara takardun neman guraben Karatu (wato scholarship) daga dalibai ‘yan asalin jihar Katsina zuwa Jami’o’in Kasashen waje wanda Gwamnatin Jiha za ta dauki nauyinsu.

Kwasa-kwasan da za a karanta sune: -
Karatun ilimin likita (wato MBBS)
Karatun ilimin kirkire-kirkiren Na’ura mai kwakwalwa dake da kaifin basira (wato Artificial Intelligence)
Karatun ilimin tattalin arziki dake da alaka da hallittu da tsirrai. (wato Bio-Economy).
Daliban da suke da sha’awar shiga shirin su kasance suna da takardu kamar haka:-
Takardar Sakamakon gama makarantar sakandare WAEC/NECO a zama guda, da yabo (wato credit) akalla takwas (8) a darussa kamar haka:-
Darasin ilimin kwakwaf (Physics)
Darasin ilimin hada magunguna (Chemistry)
Darasin ilimin sanin hallittu da tsirrai (Biology), kona Ilimin Aikin Gona (Agric Science)
Darasin Turanci
Darasin Lissafi
Darasin ilimin Na’ura Mai Kwakwalwa [a inda keda bukatar haka]
Bugu da kari, daliban da ke neman karatun likitanci (wato MBBS), wajibi ne su kasance suna da sakamako mai daraja ta “A” ko “B” akalla a darussa ukku masu alaka.
Sauran Kwasakwasan biyu kuma (wato, Artificial intelligence da Bio Economy) wajibi ne dalibi ya kasance yana da sakamako mai matakin daraja “A” ko “B” akalla guda biyu (2).
Sannan wajibi ne dalibi ya kasance bai gaza shekaru goma sha shidda (16) ba, kuma bai wuce shekaru ashirin da biyu (22) ba na haihuwa a lokacin neman wannan gurbin Karatu.    
Daliban da suka gama makarantun gwamnati kadai ne za su shiga wannan shiri.
Sannan Kowace Karamar Hukuma za ta samu wakilci a cikin daliban da za a tantance a kuma dauka.
Za a aiko da takardun neman gurbin karatun tare da: -  
Takardun shaidar gama makarantar primary da na sakandare WAEC/NECO.
Takardar haihuwa.
Takardar shaidar zama dan Karamar hukuma
Takardar shaidar nuna hali na gari mai dauke da sa hannun shugaban Karamar hukuma.
Za a aiko da takardun neman guraben karatun ga adireshi kamar haka: -
The Chairman 
Coordination committee
Special Foreign Scholarship Programme     
Katsina State.

Ana iya aikawa da takardun a ofishin shiyyar ilimi na tsofaffin kananan hukumomi 7 na : -
Katsina, Daura, Funtua, Malumfashi, Kankia, Dutsinma da Mani. Ko kuma a aiko da takardun neman gurbin karatun a sakateriyar kwamitin da ke a ofishin shugaban Ma’aikata na Jaha wanda ke Babbar Sakateriya Jahar Katsina.
Za a lika sunayen wadan da aka tantance don su zauna jarabawa, tare da wuri, da lokacin yin jarabawar, a kananan hukumomin daliban, ranar Lahadi 15 ga watan October, 2023.
Za a fara amsar takardun neman gurbin karatun daga ranar Laraba 4 ga watan October, 2023, za a kuma rufe amsar a ranar Laraba 11 ga watan October, 2023. In sha Allah.

Sanarwa daga Sakataren Kwamitin Gudanarwa, Mas'ud B. Mustapha, (Permanent Secretary, Establishment, Pension & Training).

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp