NAHCON ta ba jihar Katsina kujerun aikin hajji 4,513 a hajjin badi, 2024


Hukumar kula da aikin hajji ta jihar Katsina ta sanar cewa jihar ta samu yawan kujerun aikin hajjin shekarar 2024 kimamin 4,513 daga hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON.

Kazalika hukumar ta sanar cewa an fara biyan kudin ajiya na Naira milyan 4 da dubu 500 ga duk maniyyacin da ke da burin sauke farali a badi, 2024.

Shugaban hukumar ta kula da aikin hajji ta jihar Katsina Alhaji Sulaiman Nuhu Kuki, ya sanar cewa gwamnatin jihar ta amince da a fara rajistar maniyyata aikin hajjin badi, 2024 tare da karbar kudaden ajiya na wadannan maniyyata.

Ya yi karin hasken cewa maimakon saka kudin ajiyar na jimillar Naira 4.5, gwamnatin jihar Katsina ta saukaka, inda ta ce ko da Naira milyan uku ana iya fara ajiyewa, daga bisani a rika sanyawa kadan-kadan har su cika 4.5 din duba da yanayin tattalin arzikin da ake ciki.

Shugaban hukumar ya ce maniyyata aikin hajjin na badi na da daga nan har zuwa watan Disambar shekarar nan na su zuba kudaden ajiyar ta su na aikin hajjin.

Alhaji Sulaiman Nuhu Kuki ya ce Nijeriya gabadaya, an samu jimillar kujerun aikin hajji 95,000 daga kasar Saudi Arabia kamar yadda aka yi a shekarar nan ta 2023.

Shugaban hukumar kula da aikin hajjin ta jihar Katsina ya ce yanzu haka kuma ana nan ana ci gaba da biyan kudaden wadanda suka fara ajiye kudi a hukumar a aikin hajjin da ya gabata, amma ba su samu damar cika kudin ba, har lokacin aikin hajjin ya wuce. 

Sai ya yi kira ga maniyyata aikin hajjin da su rika muamala Kai tsaye da jami'an hukumar kula da aikin hajji don gudun fadawa hannun 'yan damfara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp