Wani mai tabin hankali ya kashe mutane 8 a Adamawa

......sai dai shi ma wasu fusatattu sun kashe shi


Wani mutum da ya samu matsalar tabin hankali ya bi mutane da sara da wuka har ya kashe 8 ya jikkata da dama a yankin Kate-Gamji na karamar hukumar Shellengbta jihar Adamawa.

Mutumin mai suna Ali Denham ya zari wukarsa ya bi mutane yana yanka har ya kashe mutane 8 ya jikkata karin uku a daren Larabar makon nan, kafin daga bisani aka samu wasu fusatattu, suka kashe shi.

Da ya ke tabbatar da lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Sulaiman Nguroje ya ja kunnen mutane da su daina ajiye masu tabin hankali a gida ba tare da sun kai su asibiti ba.

Ya ce mutumin da ke da tabin hankali ya kashe mutane 8 kafin a samu wasu fusatattu shi ma su kashe shi.


Post a Comment

Previous Post Next Post