Tsohon shugaban kasa Buhari na nadamar irin shugabancin da ya yi - Solomon Dalung


Tsohon ministan matasa da wasanni a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, Barr Solomon Dalung ya yi ikirarin cewa yanzu haka halin da ake ciki, tsohon shugaban kasa Buhari na nadamar irin shugabancin da ya yi a zamanin da ke shugaban kasa.

Solomon Dalung ya ce dalilin da na sanin da Buhari ke yo, shi ne na yadda wasu makusantansa suka ingiza shi ya aikata abin da ya aikata da yanzu ba ya jin dadin abin.

Barr Dalung da ya yi minista a wa'adin farko na gwamnatin Buhari daga 2015-2019, ya ce shugaba Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe na 2015.

A lokacin da ya ke tattaunawa da gidan rediyon Trust Radio, ya ce dole ya fadi gaskiya a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka yanke wa APC cibi.

Sai dai Solomon Dalung ya ce tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, da ya aminta da mutanen da ke kewaye da shi dari bisa dari. Sai dai yanzu haka Buhari na nadamar amincewa wadannan mutane da ya yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp