Tinubu ya dakatar da kaddamar da sabbin jami’o’i 37 da Buhari ya amince da su – Minista


Gwamnatin Tarayya ta ce za a samu jinkiri kafin sabbin jami’o’i 37 da gwamnatin da ta shude ta amince da su su fara aiki.


Ministan Ilimi Tahir Mamman ya bayyana haka jim kadan bayan ya yi wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba a Abuja.


Ministan ya ce hakan ya kasance ne bisa la’akari da bukatar za a  samar wa da jami'oin da ingantattun shirye-shirye domin bayar da ingantacen ilimi.


Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne dai ya amince da sabbin jami'oin guda 37 kwanaki kadan kafin ya mika mulki ga gwamnatin shugaba Tinubu.
Rahoto: Ahmad Rabe Yanduna/Umar Ibrahim

Post a Comment

Previous Post Next Post