Shirin Dadin-Kowa ya sa samari son yin wuf da ni - Fati Harka


Fitacciyar jaruma a cikin shirin Dadin_Kowa mai dogon zango Amina Adam Jos da aka fi sani da Fati Harka ta ce rawar da take takawa a cikin shirin Dadin_Kowa ta soyayya da kananan yara ta sanya a zahiri samari masu kananan shekaru na tunkararta da zance cewa suna son yin soyayyar gaske da ita.
Fati Harka a cikin wata hira da BBChausa ta ce duk da cewa tana da samari hakan bai sanya ta wulakanta kananan yaran da ke zuwa wajenta su yi mata lafazin cewa suna son yi soyayya da ita a zahiri ba.Rahoto: Ahmadu Rabe Yanduna/Umar Ibrahim

Post a Comment

Previous Post Next Post