Tinubu na kitsa yadda zai yi shekaru 8 amma ba za mu yarda ba - Sheikh Gumi

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1X1liesF6jCXXBiT_-zrbLy7zSEl2sBRZ
Malamin addinin Islama Sheikh Abubakar Gumi ya ce Shugaba Tinubu da mutanensa na kitsa yadda za su yi shekaru takwas a kan mulkin Nijeriya amma a cewar malamin shugaban ba zai samu biyan bukata ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito malamin a wani faifan bidiyo na fadin yadda gwamnatin Tinubu ta mayar da arewacin kasar saniyar ware. Ya ce an nada ministocin tsaro Musulmai amma a zahiri manyan sojoji da ke bayar da umurni a fagen daga ba Musulmai ba ne.

A cikin bidiyon kuma malamin ya nuna rashin jin dadinsa da kamun ludayin ministan Abuja Nyesom Wike, wanda malamin ya yi zargin na gab da mayar da Abuja matattarar Yahudawa tamkar birnin Tel Aviv.

Post a Comment

Previous Post Next Post