Shugaba Tinubu zai yi kasafin Naira Tiriliyan 26 a 2024 domin tafiyar da gwamnatin Nijeriya


Gwamnatin shugaba Tinubu ta tsara yin kasafin kudin shekarar 2024 da zai iya lakume kimanin Naira Tiriliyan 26. Kasafin kudin wanda ake sa ran mika wa majalisun kasar domin amincewa da shi kafin karshen wannan wata na Oktoba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Sai dai wannan ne karo na farko da kasar ta yi kasafin kudi mafi girma da ya kai kimanin dala bilyan 33.8 wanda ya zarta wanda gwamnatin da ta shude ta yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post