Gudun bara ko afka wa assha ya sa nake sayar da ruwa a 'kura' - Macen da ke tura kurar-ruwa a Kano


Malama Gambo Haruna, mace ce mai matsakaitan shekaru a birnin Kano da ta shafe shekaru sama da biyu tana tura kurar-ruwa domin sayar da ruwa ta samu abin da za ta ciyar da 'ya'yanta 6.

Mijin Gambo dai, ya rasu ne shekaru kusan 6 da suka gabata.

Matar na zaune ne a wani gidan da ta kama hayar daki daya, inda take biyan kudi Naira 12,000 duk shekara a Gadar Katako Rimin Kebe cikin karamar hukumar Ungoggo jihar Kano.

Binciken Daily Trust ya gano cewa matar na cikin matsanancin halin rayuwa, ganin yadda a shekarunta bai kamata ta yi wannan tsufan ba.

Malama Gambo ta ce tana yin dukkanin mai yiwuwa don ganin ta samu abin da za ta ciyar da 'ya'yanta don tana gudun ta yi bara ko shiga wata harkar da bata dace ba.

Ta yi imanin cewa duk halin da take ciki, Allah Ya sani, kuma zai fitar da ita.

Sai dai duk da wannan hali da Malam Gambo take ciki, bai hana 'ya'yanta zuwa makaranta ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post