Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu na daga cikin jerin sunayen mutane 500 musulmai da ke da karfin fada a ji a duniya.
Kazalika, akwai mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar da mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da karin wadansu 'yan Nijeriya 12 da ke cikin jerin sunayen mutanen.
Wannan ne karon farko da aka ambato sunan shugaba Tinubu a jerin sunayen musulmai masu karfin fada a ji a duniya da cibiyar kula da harkokin addini ta kasar Jordan ke fitarwa duk shekara.
Sai dai, a wannan sabon bugun, an cire sunan tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari da ya ke yawan fitowa a duk lokacin da aka fitar da sunayen.
Shekh Habib Umar Bn Muhammad Bn Salim Bn Hafiz ne Musulmin da ya fi kowa karfin fada a ji a duniya.