Farkon Kannywood, karuwai ma kyamarta suke yi - Kamaye

Sanannen marubucin nan, mai shirya fim tare da ba da umurni, Dan Azumi Baba da aka fi sani da Kamaye ya ce lokacin da aka bude masana'antar shirya fim ta Kannywood karuwai ma kyamarta suke yi.

Kamaye da aka zanta da shi a shirin Gabon Talk Show ya ce a zamanin babu macen da ke son a ga fuskarta a fim, saboda ana zaton harkar shashanci ce kawai a ciki.

Dan Azumi Baba ya ce "an yi lokacin da idan muka je gidan karuwai neman wadda za mu saka a fim, sai karuwa 'yar'uwarta ta hana, ta ce za ki shiga fim kamar dai 'yar iska".

Ya ce a zamanin, Hindatu Bashir wata tsohuwar jaruma a masana'antar ce kadai ke aminta ta fito a fim.

Post a Comment

Previous Post Next Post