Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar da a watan Janairun 2024 za a fara ba daliban kasar bashin kudin da za su dauki dawainiyar karatunsu.
Shugaban kasar da ya furta haka a a Abuja wajen taron kula da tattalin arziki, ya ce idan aka aiwatar da hakan, batun yajin aikin malaman jami'o'i zai zamo tarihi.
Shugaban kasar ya kuma yi magana sosai kan yadda gwamnatinsa ta yi tsare-tsare don ganin an saita tattalin arzikin kasar.