Wata mata mai suna Mrs Oluchukwu Nwosu ta sayar da jikanta dan watanni uku kan kudi Naira dubu 50, inda ta zargi halin matsin rayuwa da cire tallafin man fetur ya ingiza ta a Nnewi ta jihar Anambra.
Mrs Nwosu ta ce diyarta da ta haifi wannan jariri, dama ta taba haihuwar wasu biyu a baya, ta sakar mata, tana ta wahala da su, inda ta ce ba ta da karfi, yanzu haka wadancan yaran biyu na gidan marayu na Awka.
Matar na neman yafiya, sai dai ta ce tana cikin halin matsin rayuwa tun bayan da diyarta ta haihu, ba su iya cin abinci sau uku a rana.
Tochukwu Asiegbu ne dai ake zargin ya sayi wannan jariri sabuwar haihuwa. Sai dai kwamishinar mata ta jihar Anambra Lfy Obinabo ta tabbatar da cewa an ceto jinjirin da aka cefanar.