Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto ya ce babu ko sisin-kwabo a lokacin da ya karbi ragamar tafiyar da jihar a matsayin Gwamna daga hannun Aminu Waziri Tambuwal.
Kazalika, Gwamnan ya ce babu wata takardar hannanta mulki da tsohuwar gwamnati ta bashi a lokacin da aka rantsar da shi.
Gwamna Ahmad na ba da amsa ne ga mataimakin shugaban majalisar wakilai Benjamin Kanu da ya tambaye shi yadda aka yi ya iya gabatar da ayyuka kusan 100 a cikin kwanakinsa 100 da rike ragamar tafiyar da jihar Sokoto.
Benjamin Kanu dai ya ziyarci Sokoto ne a ranar Alhamis a lokacin da ya je ziyarar ta'aziyya.
Gwamnan da ya yi magana ta hannun mataimakinsa Engr Idris Gobir ya ce kawai suna sadaukar da rayuwarsu ne don al'ummar jihar Sokoto su samu saukin rayuwa, amma dai ba su tarar da sisin-kwabo a cikin lalitar gwamnatin jihar kusan watanni biyar kenan.