An rufe kasuwar Mile 12 International Market Lagos

Gwamnatin jihar Lagos ta umurci da a gaggauta rufe kasuwannin Mile 12 International Market, da Owode Onirin.

A cikin wata sanarwa daga daraktan hulda da jama'a na ma'aikatar muhalli ta jihar Kunle Adesina ta ce an rufe wadannan kasuwanni ne biyo bayan rashin tsafta da sauran karya dokokin da suka shafi muhalli.

Ya ce an rufe wadannan kasuwanni ne biyo bayan wani aikin hadin guiwa da jami'an LAWMA da na KAI suka gudanar biyo bayan umurnin da suka samu daga kwamishinan ruwa da tsaftar muhalli na jihar Tokumbo Wahab.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar Lagos ba za ta sassauta kan duk wani nau'in tara kazanta ba a ko'ina.

1 Comments

  1. Ai yakamata arufe Dan nan Gaba kafin a Bude kaga zasu rinka gyarawa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post