Za a haifi jarirai 365,595 a Jigawa cikin shekarar 2023


Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ana kyautata zaton samun haihuwar jarirai 365,595 a jihar cikin shekarar nan ta 2023.

Kwamishinan lafiya na jihar Abdullahi Kainuwa ya sanar da hakan a Dutse babban birnin jihar kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

A wajen taron, Abdullahi Kainuwa ya ce matan da suka kai shekarun haihuwa a jihar suna samun maganin hana haihuwa na zamani a akalla a cibiyoyin kiwon lafiya 300 daga cikin cibiyoyi 761 da ke jihar.

Kwamishinan ya ce daga cikin jariran 365,595, tuni har an haifi 273,000 ya zuwa watan Juli da ya gabata.

Ya ce jihar na da matan da ke iya daukar ciki su haihu kimanin 1,608,616. Sai dai ma'aikatar kula da lafiya ta jihar na kokarin nan da shekarar 2027, matan na amfani da maganin takaita haihuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp