Zulum ya kaddamar da dashen itatuwa milyan 1.2


Gwamnan jihar Borno Prof Babagana Umara Zulum ya kaddamar da dashen itatuwa na shekarar 2023, da za a dasa itatuwa milyan 1.2 a fadin jihar.

Kazalika, Gwamna Zulum ya sanar da cewa ana kyautata zaton cewa nan da shekarar badi, 2024, za a dasa itatuwa milyan 10 a jihar.


A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamna Zulum, Malam Isah Gusau da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce Gwamna Zulum ya shawarci ma'aikatar kula da muhalli da ta watsar da tsarin dashen itatuwa na dauri ta rungumi na zamani domin tafiya da zamani.

Sanarwar Malam Isah Gusau ta ce Gwamna Zulum ya kudurci aniyar dasa itatuwan ne domin yaki da kwararowar hamada da matsalolin da suka jibinci muhalli a jihar.

Kazalika, Prof Zulum ya bukaci mutane da su rage amfani da itace wajen girki don gudun gurbatar yanayi da alkinta muhalli.

Gwamnan Babagana Umara Zulum ya ce daga cikin dashen itatuwa milyan 10 da jihar ke hankoron dasawa nan da 2024, ana kyautata zaton a dasa itace 200,000 a kowace karamar hukuma 27 da ke jihar, jimilla dashe milyan 5.4 a yayin da gwamnatin jiha za ta samar da dashe milyan 5.

Post a Comment

Previous Post Next Post