Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo cewa an samu
wasu mata da ke shanyewa mutane jini a sassan jihar, ko kuma su sace musu wani
sashe na jikin su ta hanyar tsafi.
A wani gajeran bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Tik-Tok, jami’in yada
labaran rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa ya ce a rahotannin da
suka samu a unguwannin Kurna, kwana hudu, Hotoro, Zango, Rijiyar Lemo da kuma Gwagwarwa,
an kama wasu mata da ake zargin masu shan jinin ne kuma har ana yunkurin afka
musu.
SP Kiyawa ya bayar da misalin yadda lamarin ya faru a unguwar kwana hudu,
inda ya ce wasu ‘yan mata ne suka shiga wani gida don kaiwa matar gidan Chajin
waya, shigar su ke da wuya kuma sai daya ta tambayi izinin matar gidan don kama
ruwa, jin haka ke da wuya kuma matar gidan ta fara ihu, kuma ba tare da bata
lokaci ba mutanen suka far musu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan na jihar Kano ya ce tuni suka kama
mutane 8 cikin wadanda ke yunkurin daukar doka kan wadanda ake zargi da shan jini,
yana mai cewa tun daga lokacin da aka fara yada wannan jita-jita babu wanda aka
samu da rahoton an shanye masa jini ko kuma wani sassa na jikin sa ya bace
kamar yadda ake yadawa ba.
SP Haruna ya kuma bukaci jama’ar Kano da su kwantar da hankalin su yana mai
cewa wannan labari kawai an shirya shi ne don haifar da rudani, sannan ya
gargadi masu irin wannan ta’ada da su kuka da Kansu matukar aka kama su.