'Yan ta'adda sun kashe mutane 7, sun raunata 5 sun sace 11 a wani sabon hari a Katsina


Wasu mutane dauke muggan makamai da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne, sun afka kauyen Doka na karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina cikin daren Litinin wayewar Talata, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi.

Bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce 'yan ta'addar a yayin wannan harbe-harbe, sun kashe mutanen gari 7 suka raunata 5.

Wata majiya daga yankin da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce mutanen sun kuma sace wasu daga al'ummar yankin su 11 tare da kwashe dabbobin da har ya zuwa lokacin hada wannan labarin ba a kai ga sanin hakikanin yawansu ba.

Kauyen Doka dai na cikin mazabar Mai Bakko a cikin karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta hannun mai magana da yawunta ASP Abubakar Sadiq Aliyu ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce mutane 6 ne aka kashe tare da raunata 5.

Duk da rundunar 'yan sandan ba ta tabbatar da yawan mutane da dabbobin da 'yan ta'addr suka sata ba, sai dai ta ce jami'anta yanzu na can na bincike a cikin dajin da ake kyautata zaton an tafi da mutane da dabbobin domin kwato su.

ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya ce an ma kara tsaurara matakan tsaro domin ceto mutanen da kuma kare afkuwar hakan a gaba.

1 Comments

Previous Post Next Post