Bankuna da hukumomin gwamnati da ke biyayya ga kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya sun kauracewa guraren ayyukan su, yayin da yajin aikin ya doshi sa’o’I 24.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NLC ya ruwaito
cewa baki daya bankuna basu yi aiki a fadin kasar ba, yayin da wasu daga cikin
ma’aikatun gwamnati suka fita aiki wasu kuma suka zauna a gida.
Tun farko dai kungiyar NLC ce ta kuduri aniyar tafiya yajin
aikin na kwanaki biyu don nunawa gwamnatin kasar bacin ranta a game da rashin
mayar da tallafin man fetur da ya haddasa tsadar rayuwa.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce zata kuma tsunduma
wani yajin aikin na sai baba ta gani nan da makonni biyu masu zuwa matukar
gwamnati bata dauki matakin gyara bayan wannan yajin aikin da suka aiwatar ba.
DCL Hausa ta gano yadda mambobin na kungiyar NLC suka kulle
kofofin shiga gidan talabijin din NTA na kasa da na Radio don hana ma’aikata shiga.
To amma dai masana a kasar na ganin zai yi wuya
wannan yajin aikin yayi tasiri la’akari da barakar da ke tsakanin kungiyoyin
kwadago guda biyu na NLC da TUC, kasancewar TUC ta barranta kanta da mambobin
ta daga wannan yajin aiki.