Gwamnan Zamfara ya rufe wasu manyan kasuwannin shanu a jihar

Gwamnatin Zamfara ta sanar da rufe kasuwannin shanu 8 nan take a kananan hukumomi biyar na jihar.

 Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu Mannir Haidara ya fitar ranar Lahadi a Gusau.

Kasuwannin shanun da abin ya shafa su ne: Danjibga da Kunchin-Kalgo da ke Tsafe; Kasuwan shanu na Bagega da Wuya a garin Anka.

 “Sauran su ne Dangulbi da Dansadau a Maru, Dauran a Zurmi da Nasarawar Burkullu a karamar hukumar Bukkuyim.

Gwamnatin jihar ta ce ta dauki matakin ne biyo bayan sake bullar cinikayyar siyar da shanun sata da wasu da ake zargin 'yan fashin dajin ne suke yi a yankunan da lamarin ya shafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post