'Yan ta'adda sun farmaki wani masallaci sun kashe masallata a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna da ke Arewacin Nijeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Saya-Saya a karamar hukumar Ikara kamar yaddajaridarDailytrust taruwaito. 

Majiyar ta DCLHausa ta ce a yayin harin 'yan bindigar sun kashe masallata 5.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 8 na dare na ranar Juma’a a daidai lokacin da mutanen ke gudanar da Sallar Isha’i a wannan masallaci.

Mansir Alhassan shi ne 
mukaddashin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin a Asabar din nan a Kaduna.

Post a Comment

Previous Post Next Post