Gwamnatin Dikko ta raba N20m ga iyalan 'yan sintirin da 'yan ta'adda suka hallaka a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rarraba kudi Naira milyan 20 ga wasu daga cikin iyalai da 'yan'uwan 'yan sintirin Vigilante da 'yan ta'adda suka hallaka a lokacin da suke bakin daga a jihar.

Sakataren Gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari a lokacin rarraba kudin a Katsina, ya ce kudin wani tallafi ne ga iyalan mamatan ba wai diyyar rayukansu ba.

A nasa bangaren, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Katsina kan 'yan gudun hijra da wadanda iftila'i ya fada mawa Sa'id Ibrahim Danja ya ce gwamnatin ta kuma dauki nauyin kula da lafiyar duk jami'an da aka raunata a lokacin da suke kokarin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar yankunansu.

Ya ce akwai jami'an tsaro 4 da mutanen gari 32 da ke kwance a asibitin kashi na 'Orthorpaedic Katsina' da asibitin koyarwa na Federal Teaching Hospital, Katsina inda suke karbar magani da kulawar likitoci duk kyauta bayan da gwamnatin Dikko ta dauke musu dawainiyar.

Ya ce wannan tallafi an yi shi ne da zummar tallafar wadanda suka samu raunuka da iyalan wadanda suka rasu a lokacin arangama da 'yan ta'adda musamman a kananan hukumomin da ke fama da karancin tsaro a jihar.

Hon Sa'id Ibrahim Danja ya ce iyalan 'yan sintiri 33 ne suka amfana da wannan tallafin kudin, inda aka rarraba musu Naira dubu dari biyar-biyar, a yayin da wadanda suka samu raunuka su 10 suka samu Naira dubu 250 kowane.

Kazalika, akwai wani jami'in dan sanda mai mukamin 'Insfekta' da ya samu rauni aka bashi gudunmuwa kudi Naira dubu 250 sai jinjirin matar wani soja da ya rasa ransa a filin daga aka bata gudunmuwr kudi Naira milyan 1. Bayanai dai sun ce 'yan ta'addar sun hallaka wannan soja ne a ranar da ake sunan jaririn.

Post a Comment

Previous Post Next Post