Fitacciyar jaruma a masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood Aisha Humaira ta fito fili ta nuna rashin jin dadinta dangane da wani taimako da ta yi wa wani yaro masoyinta da ya zo Kano saboda ita.
Humaira ta ce bayan an kawo mata yaron ta yi masa goma ta arziki ta kuma yi alkawarin cewa za ta dauki nauyin karatunsa.
Ta ce yanzu haka yaron sau biyu tana sa a mayar da shi garinsu yana dawowa wai sai an kawo shi wajenta.
A karshe dai jarumar ta nuna cewa ta iya masa iya abin da za ta iya don haka ta mika shi ga hukumar Hisbah a jihar Kano.