Rundunar ‘yan sandan jihar Plateu ta sanar da kama wani likita da laifin sace kodar wata mara lafiya mai suna Kehinde Kamal.
Mai Magana da yawun rundunar,
DSP Alabo Alfred wanda ya tabbatarwa da manema labarai kamun, ya ce har yanzu ana
kan bincike amma tuni wanda ake zargin ya zo hannu.
Kamun na Dr Noah Kekere da ke aiki a asibitin Murma na yankin Yanshanu
na karamar hukumar Jos ta arewa ya zo ne bayan da mijin matar da aka cirewa
kodar Alhaji Kamal ya kaiwa ‘yan sanda korafi.
Alhaji Kamal ya zargi Dr Kekere da sacewa matar tasa
koda tun a shekarar 2018.
Da yake yiwa ‘yan sandan karin bayani kan yadda lamarin ya faru, Alhaji Kamal ya
ce a shekarar 2018 ne matarsa ta rika korafi da ciwon ciki, bayan ya kaita
asibitin ne kuma likitan ya sanar da su cewa tana fama da cutar Appendix, ma’ana
tsakuwa ta taru a cikin ta, inda ya bukaci yi mata aiki don fitar da su.
Alhaji Kamal ya ci gaba da cewa “Na biya kudin aiki cikakke, sai
dai bayan an yi mata aiki ne kuma sai ciwon yafi na baya tsanani haka muka yi
ta fama har tsahon shekara guda kafin muka yanke shawarar komawa gurin likitan
kasancewar shine ya san matsalar ta amma duk da haka bata daina fama da ciwo ba”
a cewar Alhaji Kamal.
Bayan da ya ga ciwo ya ki ci ya ki cinyewa ne kuma ya yanke
shawarar kaita asibitin koyarwa na jami’ar Jos, inda aka tabbatar masa da cewa
matar bata da koda daya.
Yace “Da farko ban yarda ba,
sai da na kaita wani asibiti mai zaman kansa inda nan ma aka tabbatar min da
cewa koda daya ce da ita”.
“Ni abinda nake so kawai ayi min adalci, ina son duniya ta san halin da
matata ke ciki”
Tuni dai yanzu aka dauke likitan daga ofishin ‘yan sanda na yankin Gwom zuwa
shalakwatar ‘yan sanda ta jihar.