Matasan Jigawa sun tarwatsa gungun 'yan fashi


 

Bayanai daga kauyen Tage da ke karamar hukumar Kafin Hausa ta jihar Jigawa na cewa matasan Kauyen sun takawa wani yunkurin aikata fashi da makami birki akan babbar hanyar Hedejia.

Rahotanni sun bayyana cewa tun farko ‘yan fashin sun fara tare babbar hanyar Hadejia don yiwa matafiya hari, sai dai ba tare da bata lokaci ba matasan kauyen suka yo zuga dauke a matakami kuma suka tunkari gungun ‘yan fashin.

Bayan gwabazawa da juna ne kuma ‘yan fashin suka yanke shawarar tserewa duk da cewa matsan sun kama guda daga cikin su.

Wani ganau ya shaidawa jaridar Punch cewa matasan sun daddatsa sassan jikin dan fashin da suka kama da adda.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Jigawa Lawan Adam yace jim kadan bayan fara arangamar tsakanin matasan da ‘yan fashin ne  ‘yan sanda suka isa wajen, nan ne kuma suka yi nasarar karbar dan fashin mai suna Abudullahi Abubakar mazaunin kauyen Hago na karamar hukumar Kafin Hausar kafin matasan su kai ga kashe shi.

A cewar sa ‘yan sandan sun yi nasarar kwato harsasai da kudi har naira miliyan 37 a hannun ‘yan fashin.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post