Yakin bai kare ba- Atiku Abubakar


 

Dan takarar shugaban Najeriya karkashin Inuwar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya sake jadadda watsin da ya yi da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe, da ya tabbatar da Bola Tinubu a matsayin halastaccen shugaban kasar.

 

Yayin wani taron manema labarai da ya yi da yammacin yau a birnin tarayya Abuja, Atiku Abubakar ya ce “Yakin bai kare ba” a cewar sa babu wata-wata zai garzaya zuwa kotun koli.


A wajen taron manema labaran, Atiku Abubakar ya fito karara ya bukaci lauyoyinsa da su yi gaggawar shigar da kara kotun koli sannan su fara tattara hujjoji.

“ Ni ba bakon shari’a bane, don haka taron lauyoyi da babaken dogayen riguna ba zai razana ni ba, kuma idan ka bi tarihin siyasa ta na kasance dan gwagwarmaya da bana barin ta kwana, don haka zan yi duk mai yiwuwa don kwato abinda dama nawa ne a gaban shari’a” inji Atiku Abubakar.

Atikun ya kuma ci gaba da cewa wannan yakin ba don biyan bukatun sa dari bisa dari yake yi ba, a’a don tilastawa hukumar zaben kasa mai zaman kanta INEC ta daidaita sahun ta, ta kuma gane cewa kotu tana da karfin tayar da hukuncin zalunci da ta yanke.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp