APC A jihar Katsina ta taya 'yan takararta murnar samun nasara a kotu

 Shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu Daura ya taya yan takarar jam'iyyar murna bisa nasarar da suka samu a kotun sauraren kararrakin zaɓe (Election Tribunal) yana mai bayyana hakan a matsayin nasara ga jam'iyyar APC da magoya bayanta

Yan takarar da suka samu nasarar a hukuncin daban-daban wanda kotun ta zartas sun haɗa da Honarabul Sani Aliyu Ɗanlami na mazabar majalisar tarayya ta karamar hukumar Katsina da Honarabul Abubakar Yahaya Kusada na mazabar Kankia/Kusada/Ingawa wadanda kotu ta maido masu da nasarar su a babban zaben watan Fabrairun 2023 da ya gabata tare da soke zaben yan takarar PDP da aka bayyana a farko a matsayin wadanda suka samu nasara.


Akwai kuma yan majalisun tarayya na Mazabar Ƙanƙara/Faskari/Sabuwa da Batsari/Safana/Danmusa waɗanda kotun zaben ta bayyana zabukan su a matsayin wadanda basu cika ba tare da bada umarni a sake zaben a inda aka bayyana

 Da yake tsokaci akan nasarar, shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina, Sani Aliyu ya bayyana cewa magoya bayan APC  sun yi bakin kokarin su domin wannan nasara a lokacin zaben, yana mai cewa hukuncin kotun ya tabbatar da muradin dubban al'ummar mazabun wadanda suka fita suka jajirce wajen 'kada ma yan takarar jam'iyyar APCn kuri'un su

  "Magoya bayan mu sun bayyana muradin su ta hanyar kuri'un su kuma gashi yanzu yar gwadal ta nuna cewa lallai yan takarar APC suka ci zabe kuma tun akwatunan zaben,"

 "Abinda muke shedawa a yanzu shine kyawun tsarin Demokradiya da kuma mahimmancin bin doka da oda, mun ce anyi mamu ba dai dai ba, mun kai koken mu inda ya dace, kuma gashi an share mamu hawayen mu, muna jinjina ma adalcin bangaren shari'a.

 "A madadin jam'iyyar mu ta APC a jihar Katsina Ina taya yan majalisun mu murna bisa wannan nasara da suka samu a kotu wanda ya tabbatar da cewa Katsina ta APC ce,".inji shugaban jam'iyyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp